Tuesday, 29 October 2019

Kalli hotunan irin kwanciyar Ruf da ciki da Neymar yayi akan Mahaifiyarshi data jawo cece-kuce sosai

Tauraron dan kwallon Brazil me bugawa kungiyar PSG wasa,Neymar Kenan a wannan hoton inda yake tare da mahaifiyarshi inda aka ganshi ya kwanta akan bayanta, Neymar dinne ya saka wannan hoto a shafinshi na sada zumunta kuma ya dauki hankula.
Watakila dai a kasar Brazil wannan abu da Neymar yayi ba abin Magana bane amma a sauran sassan Duniya da dama wannan abu zai zamarwa mutane banbaraakwai.

Ba wannane karin farko da Neymar din ke yin abinda mutane ke ganin be dace da mahaifiyar tashi ba, koda kusan watanni 8 da suka gabata, lokacin yana jinya, an ga wani bidiyo da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda Neymar din yana kwance a akan gadon Asibiti aka ga yana shafa mazaunan mahaifiyar tashi sannan daga baya ya daketa akansu.

Kuma bata nuna alamar damuwa ba shima wancan abu ya jawo cece kuce.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment