Wednesday, 9 October 2019

Kalli yanda jama'ar gari suka daure magajin garinsu a jikin mota suna janshi a kasa saboda be cika musu alkawarin daya dauka ba

Wani hoton bidiyo da ya nuna magajin garin Las Margaritas dake kasar Mexico me suna, Jorge Luis Escandón Hernández ana janshi a kasa ya dauki hankula sosai a shafukan sada zumunta.Jama'ar garinne suka je har ofishin magajin garin suka fito dashi suka kulleshi a jikin mota suna ja a kasa saboda bai cika musu alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe ba.

'Yansanda sun tseratar dashi sannan an kama mutum 11 da ake zargi da wannan aika-aika.

Kalli bodiyon a kasa:Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment