Saturday, 12 October 2019

Kalli yanda Sarkin Kano ya zubar da kwalla saboda wata mata da danta ya mutu sanadiyyar rashi kudin da zata kaishi Asibiti

Me martaba Sarkin kano,Muhammadu Sanusi na II ya zubar da hawaye kan labarin wata mata da ya bayar da danta ya mutu a kafadarta saboda bata da Naira Dubu 2 da zata kaishi asibiti.
Bidiyon da ya fito daga Channels ya nuna Sarki Sanusi yana jawabi a wajan wani taron majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Legas kan cimma muradun karni.

Ya bayyana cewa yana zaune a fada sai ya ji hayaniya a waje. Nan ya aika a gano mai menene ya faru. Wanda ya aika ya dawo idonshi cike da kwalla inda ya shaida cewa wata matace danta ya mutu a kafadarta.

Sarkin yace akwai wanda suka zo suna neman taimako kuma suna kan layi. Matar na daga cikin wanda suke kan layin kuma tazo ne daga wani asibiti dake kusa da fadar. Kamin a zo kanta sai dan nata ya mutu.

Sarki sanusi ya bayyana cewa Dala 5 ce ta hana matar kai danta Asibiti, yana cikin magana sai kwalla suka zubo masa. Sarkin ya kara da cewa irin abinda ke faruwa a kasarnan kenan.

Kalli bidiyon a kasa:
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment