Saturday, 19 October 2019

Kalli Yanda Wani Matashi dan Kano ke kera Jiragen Sama dana Ruwa

A TAIMAKI RAYUWAR MATASHIN INJINIYA

SALEEM matashin Dalibi ne a Kwalejin Fasaha ta jihar Kano (Kano State Polytechnic), Allah Ya ba shi baiwar kirkirar na'urorin fasaha da kimiyya na ZAMANI.
A yayin da SIRRINSU MEDIA ta ziyarce shi ya bayyana abubuwan mamaki da suka hada da jirgin yaki na ZAMANI, abin hangen nesa, na'urar ganin kananan halitta, wanda ke iya bambance tsakanin Namiji da Macen Sauro da jirgin kasa da na RUWA.


Saleem ba shi da gata da ya wuce na baiwar da Allah ya yi masa, yana matukar mararin fadada iliminsa a kasashen ketare don ci gaba da kirkirar sabbin abubuwan.

Don Allah 'yan siyasa da kungiyoyi da mawadata da gwamnatin jiha da ta tarayya a taimaki Rayuwar wannan matashin injiniya.
Daga Maje El-Hajeej HotoroKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment