Pages

Sunday 20 October 2019

Kalli yanda 'yan wasan wata kungiyar kwallon kafa a Mexico suka yi tsayuwar mintuna 3 bayan take wasa suka bari aka ci su kwallaye 2 saboda su nuna bacin ransu kan rashin biyansu hakkokinsu

A ranar Juma'ar data gabatane 'yan wasan wata kungiyar kwallon kafa a kasar Mexico, Veracruz suka tsaya cik suka ki buga wasa na tsawon mintuna 3 duk da cewa an take kwallo inda suka bar abokan wasan nasu, Tigers suka ci kwallaye 2-0.





'Yan wasan sun yi wannan abune dan nuna bacin ransu kan rashin biyansu hakkokinsu da ba'a yi ba.

Golansu yana kallo aka rika cin kwallayen shima be yi kokarin tarewa ba.


Bayan mintuna 3 ne sai suka ci gaba da wasa amma duk da haka sai da aka kara musu kwallo ta 3, saidai kamin a tashi suma sun saka kwallo 1.

Da farko dai duka kungiyoyimne suka tsaya cik inda suka ki buga wasa na tsawon minti 1 amma daga baya sai Tigers suka fara kwallo inda suka ci kwallaye 2.

Bayan kammala wasan a hirar da aka yi da 'yan kungiyar, Kyaftin din Tigers ya bayyana cewa sun amince zasu goyi bayan Veracruz akan wannan abu amma minti daya kawai suka yi da su za'a yi. Yace bayan an shiga filine sai suka ce musu mintu 3 suke so a yi shi kuma baya tunanin sauran 'yan wasan zasu amince dan hakane kawai suka ci gaba da kwallonsu.

Shi kuwa Kyaftin din Veracruz cewa yayi Tigers suna sane da cewa mintuna 3 zasu yi a tsaye kuma sun amince suma zasu tsaya amma suka ci amanarsu.



Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment