Wednesday, 9 October 2019

Kano Ce Jahar Da Ta Fi Masu Yawan Matsakaiciyar Rayuwa A Najeriya

A farkon makon nan ne,wata kungiyar Majalisar Dinkin Duniya mai bincike da bin diddigin alkaluma da suka shafi talauci a tsakanin al’umma, wato UN Global Multi-dimensional Poverty Index, ta fitar da wani rahoto da ke nuna jihar Kano ce ta fi kowace jiha a adadin masu matsakaiciyar rayuwa a Najeriya. Sai dai wasu 'yan jihar na ganin rahotan ya ci karo da yanayin zahiri na halin rayuwar al’ummar Kano.


Baya ga haka jihar ta Kano na cikin jerin jihohi a Najeriya dake kan gaba ta daukar wadatar tattalin arziki, inji rahotan na kungiyar ta UN Global Multidimensional Poverty Index.

wasu ‘yan jihar Kano sun mayar da martani game da rahoto na kungiyar Majalisar Dikin Duniya, inda suka ce ba su gamsu ba, wasu kuma sun ce sun gamsu.

Malam Kabiru Saidu Sufi, wani masani a fagen gudanar da binciki domin fito da alkaluman lamuran da suka shafi rayuwar jama’a ya yi tsokaci game da wannan rahoto.

Hakan dai na zuwa a daidai lokacin da Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin badi ga zauren Majalisar Dokokin Najeriya na sama da naira triliyon 10, wanda ake fatan zai baiwa ‘yan kasar damar cimma mizanin matsakaiciyar rayuwa ko ma zarce haka.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment