Tuesday, 15 October 2019

Kasar da ba a san ATM ba kuma layin waya yake tamkar gwal

Ana bayyana Eritrea a matsayin kasar da ta fi kowacce kama-karya a Afrika, inda mutane basu da 'yancin siyasa da kuma na addini.


Hakan ba abin mamaki ba ne don jam'iyya daya ce ta kankane komai, wato jam'iyya mai mulki ta shugaba Isaias Afwerki, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta a shekarar 1993.

Gwamnatin ta haramta kafa jam'iyyun adawa da kafafen watsa labarai masu zaman kansu, haka kuma ana daure masu sukar gwamnati ( wadanda wasu daga cikinsu an shafe shekaru ba a kara jin duriyarsu ba), sannan ta tilasta wa matasa shiga aikin soja.


Layin waya tamkar gwal yake


Wannan lamari ya janyo daruruwan 'yan Eritrea na tserewa daga kasar, kuma wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu a yayin ratsawa ta Sahara, tafiyar da ke cike da hadari ko kuma wajen tsallaka tekun Bahar Rum don zuwa nahiyar Turai.

Wakilin BBC na sashen Amharic, Jibat Tamirat ya ziyarci kasar a baya-bayan nan, karkashin sa idon wasu mutanen gwamnatin.

Ga abin da ya rubuta kan yadda gwamnatin ke matukar juya akalar al'ummar kasar.


Kamfanin sadarwa na EriTel mallakar gwamnati shi kadai ne hanyar sadarwa a kasar, kuma ayyukansa basu da inganci.

Wani rahoto na kungiyar sadarwa ta kasa da kasa ya ce, hanyar sadarwa ta intanet sama da kashi daya cikin dari ne kawai ake samu a kasar.

Don haka layin waya ya zamo tamkar gwal a kasar, inda har sai mutum ya nemi izini daga karamar hukuma kafin ya samu.

Kuma ko da ka samu layin wayar, ba zaka iya amfani da shi ba ka shiga intanet don ba a samu intanet a kan waya.

Mutane na samun intanet ne ta hanyar WiFi, sai dai bashi da sauri.

Haka kuma idan mutane na son shiga shafukan sada zumunta kamar Facebook ko Twitter, sai dai su yi amfani da wata manhaja ta (VPN) don kaucewa sa idon gwamnati.

Saboda wuyar da ake ci kafin samun layin waya, ya sa mutane har yanzu sun fi dogara a kan wuraren kiran waya na gwamnati.

Wakilan BBC sun yi amfani da irin wadannan wuraren kiran wayan a kwanaki hudu na farkon da suka yi a kasar, kafin su samu layin waya kwaya daya da suka yi amfani da shi su uku.

Wanda kuma sai da suka mayar da layin wayar kafin su bar kasar.

2) Mutane suna iya ciran kudi ne kawai a banki


Gwamnati ta takaita yawan kudaden da mutane za su iya zubawa ko cirewa daga asusunsu na banki.

Ko da kuwa suna da miliyoyin kudin kasar, nakfa a asusunsu, ba za su cire abin da ya wuce 5,000 ($330) a wata ba.

Wani mutumin da tawagar BBC ta hadu da shi a babban birnin kasar, Asmara, ya shaida musu cewa idan za ka sayi mota kirar Toyota Corolla 1986, sai ka kwashe tsawon watanni 11 kana cire nakfa 5,000 daga banki.

Sannan ka baiwa mai sayar da motar nakfa 55,000 na takardun kudi a hannunsa, ka kuma tura wani 55,000 din ta banki.

Ya ce gwamnati ta fi son a tura baki daya kudin ta banki, amma wasu 'yan kasuwan sun fi so ka basu kudin a hannu saboda babu su sosai.

Sai dai ta fuskar bukukuwan aure batun ya sha bamban, domin ana kashe kudi sosai har sama da nakfa 5,000 a wajen aure.


Idan an kusa biki sai mai daukar nauyi bikin ya je ofishin karamar hukuma don samun wata takarda daga jami'an hukumar, wanda za a kai banki don a bashi izinin ya cire fiye da nakfa 5,000 daga asusunsa.

'Yan kasar sun bayyana ra'ayoyi daban-daban kan dalilan da suke ganin yasa gwamnati ta takaita yawan kudaden da mutum zai iya cira a banki .

Wasu sun ce ''don taimaka wa mutane su saba da adani da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki ''yayin da wasu kuma ke ganin ''Gwamnati ba ta son harkar kasuwanci, shi yasa ta takaita yawan kudin da ke hannun mutane."

Babu injin cire kudi na ATM a Eritrea. Mai sayen motar ya shaida wa BBC cewa lokacin da kasar Habasha ta bude bakin iyakarta a bara, bayan kawo karshen rikicin da ke tsakaninta da Eritrea, ya je birnin Mekelle da ke arewacin Ethiopia, abin ya bashi mamaki matuka saboda yadda ya ga mutane na cire kudade masu yawa sosai daga ATM.

3) Gidan Talbijin daya ne kawai a kasar


Gidan Talbijin na Eri-Tv shi kadai ne a kasar Eritrea. Kuma shi ake amfani da shi a matsayin kafar da ke yada batutuwan da suka shafi gwamnati. Sai dai al'ummar kasar na iya kallon talbijin na waje kamar su BBC da ta Asene TV da ERISAT da wasu 'yan siyasar da ke gudun hijira a waje ke nunawa.

Kwamitin 'yan jarida na (CPJ) ya duba batun 'yancin kafafen watsa labarai a kasar, inda ya bayyana shi a matsayin kasar da ta fi kowacce sanya ido a kan mutanenta a duniya bayan kasar Koriya ta Arewa.

Kwamitin ya ambato makarantar horarwa kan watsa labarai ta Jamus wato Deutsche-Welle Akademie na cewa "a wasu lokuta ana dakile abubuwan da gidajen radiyo mallaka masu gudun hijira ke watsawa daga wajen kasar ta hanyar rashin ingancin intanet din da gwamnati ke sanya ido".

Sai dai, ministan yada labarai na kasar, Yemane Meskel ya musanta cewa Eritrea "kasa ce da ake mata kulle". Inda ya yi nuni da cewa fiye da kashi 91 cikin dari na gidajen da ke garuruwa da biranen kasar suna da tauraron dan'adam wanda ke nuna gidajen talbijin na kasashen waje fiye da 650. Inda har ma ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na twitter don tabbatar da abin da yake fada.

5) Matasa da dama na son yin kaura

''Samun fasfo tamkar burin mutum ne ya cika,'' A cewar wani matashi da ya ci abincin dare da wakilan BBC ke nan.

Amma ya ce ba a bai wa matasa fasfo har sai sun kammala bautar kasa - wanda ya hada da samun horon soji , kuma sai sun samu takardar goyon baya daga ofishin karamar hukuma.

"Sai dai sannan ka kai shekaru 40 ko 45 ka yi aure ga mata da yara," ya fada cikin barkwanci.

Kuma idan suka samu fasfon ba za su iya barin kasar ba sai sun samu bizar fita. Sannan babu tabbacin samun bizar saboda gwamnati na storon idan sun bar kasar ba za su dawo ba.

Don haka matasa da dama suna barin kasar ne ba a hukmce ba, inda suke tsallaka bakin iyakar kasar da Habasha da kuma Sudan da ba a sanya iod a kai.

Yayain da wasu kuma ke nikargari su yi tafiya mai cike da hadari ta hanyar ratsawa ta cikin Sahara shiga cikin hadari da kuma ketara tekun Bahar Rum don zuwa nahiyar Turai , inda yunwa da kishin ruwa ke kaashe su a cikin shara ko kuma su nutse a teku.


Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Eritrea ita ce kasa ta tara da aka fi samun 'yan gudun hijira a duniya, inda a karshen shekarar 2018 an samu 'yan gudun hijira 507,300 daga kasar. Abin da ke nuna cewa an samu karuwarsu da 486,200 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabace ta.

6) Sai dai babban birnin kasar na da kyau

Shugaban kasar Italiya mai kama karya, Benito Mussolini ya so Asmara ta zamo wata karamar Roma ta Afrika, a lokacin da yake shirin kafa sabuwar daula Romawa a shekarun 1930.

Manyan titunan birnin da aka kawata gefensu da shuke-shuke da gine-gine na zamani na tunawa mutum mulkin mallakar da Italiyawa suka yi wa kasar.

Duk da matsalolin tattalin arziki da na siyasa da Eritrea ke fuskanta, Asmara birni ne mai kyaun gaske da mutum zai ji shawarar kai ziyara.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment