Saturday, 12 October 2019

Kasuwar hannayen jarii ta farko a duniya

Garin Aizanoi ya na da nisan kilomita 58 tsakaninsa da birnin Kutahya. Ana kiran garin da sunan “Efes na biyu” sabida yawan kayan al’adu da yake da shi. A shekarar 1824 aka gano tsohon garin inda aka fara gudanar da ayyuka tun daga shekarar 1970.


Tsohon garin na dauke da Gidan Ibadan Zeus, gidan wasan kwaikwayo mai daukan mutane dubu 20, gidan wasanni mai daukan mutane dubu 13 da 500, gidan wanka na “hamam” guda 2, manyan hanyoyi, gadoji guda 5 da abubuwa da dama. Daya daga cikin gidajen dake garin kuwa ita ce ginin kasuwar hannayen jari. Tone-tone ya gano cewa an yi gidaje a garin a shekara ta 3000 kafin Haihuwar Annabi Isa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment