Thursday, 10 October 2019

Ko kun san alfanun shan ruwan tumatur ga maza?

Sinadarin Lycopene - da ake samu a cikin tumatur ka iya zama wata hanya ta samun waraka daga rashin haihuwa da kuma samun karin yawan ruwan maniyyin da namiji, kamar yadda wani bincike ya gano.


An gano cewa lafiyayyun mutanen da suka sha ruwan tumatur cokali biyu a rana sun fi damar sanya mace ta dauki ciki.

Matsalar rashin haihuwa da maza ke fama da ita na shafar fiye da rabin ma'aurata.

Kwararru kan kuzari na cewa akwai bukatar gudanar da wasu karin bincike da zai kunshi mutanen da ba sa haihuwa.
Hukumar Insorar lafiya ta Burtaniya ta NHS ta shawarci maza da ke da matsalar rashin haihuwa da su rinka cin abubuwa masu lafiya sannan kuma su daina sanya matsattsun kamfai.

Sannan nazarin ya shawarci masu matsalar da su rage duk wani abun da ke sa su shiga damuwa da kuma tabbatar da suna yin jima'a a kai- a kai a dai-dai lokacin da mahaifar abokiyar zamansu ke shirin daukar ciki.

To sai dai batun cewa wasu nau'in abinci ko kuma sinadari na kara damar waraka daga rashin haihuwa.

Sinadarin Lycopene wani nau'in sinadari ne da ke yi wa jikin dan adam garkuwa daga samun illa.

Har wa yau, wannan sinadari na Lycopene na rage hadarin kamuwa da matsalolin zuciya da kansa.


Masu nazarin sun ce maza na bukatar su sha kilogiram biyu na tumaturin da aka dafa a kullum domin samun kwatankwacin sinadarin lycopene.

Yadda aka gudanar da bincike
A makonni 12 da aka kwashe ana binciken, an zabi mutum 60 inda aka umarce su da su dauki miligram 14 na sinadarin lactolycopene a kullum.

Daga nan ne aka yi gwajin ruwan maniyyinsu a farko da bayan makonni shida da kuma a karshen nazarin da aka yi bai nuna wani banabanci ba dangane da yawa da lafiyar maniyyin. Sai dai an gano cewa maniyyin masu shan lycopene ya fi ninkaya a kan na wadanda ba sa sha.

Dr Liz Williams, kwararriya ce a fannin abinci a jami'ar Sheffield wanda ya jagoranci nazarin da aka buga a mujallar abinci ta nahiyar Turai, ya ce "a yanzu shawarar da za mu bayar kalilan ce."

"Muna fada musu su guji shan giya sannan su ci abinci mai inganta lafiya amma dai wadannan sakonni ne ga kowa."

Andrew Drakeley, wanda darakata ne a asibitin mata na Liverpool, ya ce "mata da maza da ke inganta rayuwar aure musamman ta hanyar neman haihuwa to su guji kashe makudan kudi wajen neman waraka."
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment