Saturday, 12 October 2019

Kotu ta tabbatar da Sauke Sanata Dino Melaye inda tace a sake zabe: Ya koma Shirin Fim

Kotun daukaka kara dake babban birnin tarayya, Abuja ta tabbatar da sauke Sanata Dino Melaye daga mukaminshi na sanata a hukuncin data yanke,jiya, Juma'a inda tace a sake zabe.
Kotun tace zaben da aka wa Sanatan Melaye baya kan ka'ida kuma ta bada Umarnin a sake zaben nan da kwanaki 90.

Da yake mayar da martani akan hukuncin kotun, Melaye yace shi be damu ba, saboda wannan hukuncin mutum ne, shi da Allah ya dogara kuma zai ci gaba da harkokinshi.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi kuwa ya bayyana cewa wannan hukuncin kotun ya tabbatar da abinda ya fada na cewa dama can zaben da akawa Melaye baya kan ka'ida.

Sanata Dino Melaye ya fito a wani shirin fim da aka shirya kan samar hakkin mutane da yun adalci a Afrika.

Da yake magana akan fitowar da yayi a cikin shirin fim din yace dama can shi ya taba shirin fim a lokacin da yake bautar kasa kuma ya ji dadin fitowa da yayi a fim din saboda ya bada gudummuwa wajan samar da 'yanci da kuma fayyace gaskiya.

Melaye yace ifan ya sake samun damar yin shirin fim din zai shiga.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment