Tuesday, 8 October 2019

Labarin komawar tsabar kudi miliyan dari 9 takardu a ofishin EFCC:Hukumar ta mayar da martani

Wani labari ya rika yawo a shafukan sada zumunta cewa wasu kudi da yawansu ya kai Naira Miliyan 900 dake ajiye a ofishin EFCC sun bce inda suka koma takarda. Saidai a sanarwar data fitar, EFCC ta karyata wannan lamari.
EFCC tace wadannan kudi tun shekarar 2015 aka kawo mata rahotonsu kuma wadanda ake zargi akan wannan kudi maganarsu na kotu. Ta kara da cewa kudin ba'a ofishinta suke ba suna CBN ne kuma taje dan duba kudin amma ta tarar an tabasu.

Sanarwar ta kara da cewa an kama wadanda ake zargi da hannu a lamarin kuma za'a yi bincike. Dan haka maganar kudi sun koma takarda a ofishinsu ba gaskiya bane
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment