Tuesday, 29 October 2019

Lacazette da Aubameyang zasu bar Arsenal saboda rashin tabuka abin arziki na kungiyar: Yanda Man United ta ki sayen Aubameyang tayi zaben tumun dare

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na fuskantar fargabar rasa manyan 'yan wasanta 2, Aubameyang da Lacazette dalili kuwa a ganin 'yan wasan Kungiyar bata tabuka abin azo a gani.
Independent ta kasar Ingila ta bayyana cewa, 'yan wasan biyu na shirin barin Arsenal ne muddin a kakar wasan bana ta kasa kaiwa ga gasar Champions League.

Arsenal dai na matsayi na 5 ne akan teburin Premier League kuma akwai tazarar maki 4 tsakaninta da ta 4. A bara Arsenal ta barar da damar kaiwa ga gasar Champions League bayan da ta yi rashin nasara a hannun Chelsea a wasan karshe na gasar cin kofin Europa da ci 4-1.

Aubameyang yace ci kwallaye 9 a wasanni 12 da ya bugawa Arsenal kuma shekarunshi 30 sannan yana gan ganiyar bajintar kwallonshi, ba zai so zama a kungiyar da ba zata haskakashi sosai yanda ya kamata ba.

Hakanan Lacazette a kakar wasan data gabata ya ciwa Arsenal kwallaye 19 a dukkanin wasannin da ya buga duk da yayi fama da jiyya shi kuma shekarunshi 28 inda shima yana kan ganiyarshi ne. Wasu rahotanni sun bayyana cewa Arsenal na shirin baiwa wadannan 'yan wasa kwantiraki me romo dan basu damar tsayawa a kungiyar.

Aubameyang Man United ya so komawa tun yana Dortmund amma Man United din ta yi watsi dashi inda ta sayi Lukaku a maimakonshi, saidai Irin kokarin da Aubameyang yayi a Arsenal Lukaku be yi irinshi a Man United ba.

Dan kuwa Aubameyang ya ciwa Arsenal kwallaye 49 a wasanni 76 da ya buga mata shi kuwa Lukaku ya ciwa Man United kwallaye 42 a wasanni 96 da ya buga mata sannan Man United ta sayi Lukaku akan Fan Miliyan 75 yayin da Arsenal ta sayi Aubameyang akan miliyan 56.

Lukaku dai ya bar Man United zuwa Inter kuma ga dukkan alamu ya fi taka rawar gani acan.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment