Friday, 11 October 2019

Masu Garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun karbi kudin fansa Biliyan 3 a hannun mutaneRahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa masu garkuwa da mutane a jihar sun karbi kudin fansa a hannun jama'ar gari da suka kai Zunzurutun kudi har Naira Biliyan 3.Wannan na kunshene a cikin rahoton da kwamiti da gwamnan jihar, Bello Matawalle ya kafa dan yin bincike akan lamarin rashin tsaron jihar da kuma itin matsalar da ya jawo.

An yi bincikenne daga shekarar 2011 zuwa 2019. Rahoton yace an karbi kudin fansa daga hannun mutane 3672.

Ya kara da cewa Mata 4983 sun rasa mazajensu a rikicin sannan yara 25, 050 sun zama marayi kuma mutane 190, 340 sun rasa muhallansu a jihar sanadiyyar hare-haren.

Ya kara da cewa fulani makiyaya sun rasa shanu 2, 015 da Tumaki da akwaki 141 da kuma rakuma da jakai 2,600 dannan 147,800 ababen hawane aka kona.

Kwamitin ya baiwa gwamna shawarar hadin kai da jihohi makwabta wajan samar da tituna da tsaro da kuma ci gaba da yin sulhu dan karbe makaman dake hannun 'yan ta'addar da kuma saka matakai dan ganin hakan bai sake faruwa ba nan gaba.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment