Saturday, 12 October 2019

Masu Garkuwa da mutane sun sako Kansila da matarsa da 'yarsa, 'yar shekara 1 bayan kwashe kwanaki 9 a hannunsu a Katsina

'Yan bindigan da suka sace kansilan Karamar Hukumar Kurfi, Mai wakiltar Mazabar Barkiya, Hon. Gambo Samaila Mai Ritaya 'Yar Liya'u, tare da matarshi da diyarsa 'yar Shekara daya, bayan kwashe kwanaki tara a hannun masu garkuwa da mutanen.


Shugaban Karamar Hukumar Kurfi, Jabiru Abdullahi Tsauri, ya kawo su da yammacin yau, ga Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari, inda ya ce sauran guda biyu da aka kubuto yanzu haka suna Asibitin Karamar Hukumar Kurfi, domin duba Lafiyarsu, Saboda halin damuwa da suka shiga.

Da Yake jawabi Gwamnan Masari, ya ce nan da Dan lokaci kadan ba zaa Kara samu kowa ba, hannun masu garkuwa da mutanen Saboda duk an sako su, sakamakon sulhun da aka yi da Yan bindigar Kuma suna cika alkawarin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment