Saturday, 12 October 2019

Matashin da be kai shekaru 20 ba ya yiwa tsohuwa me shekaru 50 fyade a Kano

Kotun Magistre dake Kank a jiya Juma'a ta saurari karar wani matashi da be kai shekaru 20 da haihuwa ba da ya aftakawa wata tsohuwa 'yar shekaru 50 a mata fyade.Alkalin kotun ya bayar da umarnin ci gaba da ajiye Babangida Inusa a gidan Yari nan da zuwa December 12 lokacin da za'a ci gaba da sauraren shari'ar.

Inusa ya fitone daga Kauyen Falgore dake karamar hukumar Kabo a jihar ta Kano.

Rabiu Hussainine ya kai karar Inusa Ofishin 'yansanda dake Garo inda yace matashin ya Afkawa tsohuwarne yayin da take gonarta
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment