Tuesday, 8 October 2019

Matashin Da Ya Yi Mafarkin Gwamna Elrufai Ya Soma Farin Jini, An Ba Shi Kyautar Sabon Babur

Matashin nan mai suna Nazifi Zubairu wanda aka fi sani da Zuri, wanda ya bayyana cewa ya yi mafarkin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Elrufai ya soma samun farin jini a wasu sassan kasar nan, inda yake ta shan kiran daga wasu jihohi da suka hada da Kano, Kaduna Lagos, Katsina, Niger, Zamfara, Sokoto, Abuja da sauran su domin jin irin mafarkin da ya yi kan gwamnan.Matashin ya ce irin kiran da ya amsa daga jihohi daban-daban na fadin kasar kan lamarin ya tabbatar masa da cewa Gwamna Elrufai yana da masoya da dama a ciki da wajen jihar Kaduna.

Tuni dai wasu daga cikin masoyan gwamnan suka soma yi masa alkairi, inda a yau din nan wani da ya nemi ya boye sunansa ya ba shi kyautar babur sabo fil.

Matashin ya kara da cewa har zuwa yanzu dai bai yi ido hudu da Gwamna Elrufai ba.

Ga lambar matashin: 08069413640Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment