Wednesday, 9 October 2019

Mutum hudu sun nutse a ruwa wajen daukar selfie a Indiya

Wata amarya da 'yan uwanta uku sun nutse a wata madatsar ruwa a lokacin da suke kokarin daukar hoton 'selfie', in ji 'yan sanda a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya.


Wadanda suka mutun dai na cikin wasu mutum shida da suka rike hannu suka shiga cikin ruwan da ya kai kugunsu a kusa da madatsar ruwan Pambar, kafin daya daga cikinsu ya zame kuma ya ja sauran suka fada ruwan.

Mijin matar ya yi nasarar ceto kanwarsa amma sauran sun nutse.
Indiya ce kasar da ta fi yawan mutanen da suka mutu yayin daukar 'selfie' a duniya.

A cewar wani rahoton dakin adana litattafan lafiya na Amurka, Indiya ce ke da rabin mutane 259 da aka san da mutuwarsu tsakanin shekarar 2011 da 2017. Daga ita sai Rasha da Amurka da Pakistan.


A Tamil Nadu ranar Lahadi, mata da mijin matasa 'yan Bargur da ke Krishnagiri sun kai wa dangi ziyara a Uthangarai tare da 'yar uwar angon, kamar yadda jaridar The Hindu ta ruwaito.

Su ukun sun shiga ruwan tare da wasu 'yan uwa uku matasa, sai daya daga cikinsu wani yaro mai shekara 14 ya zame.

Daga nan sai ya janyo 'yan uwansa mata masu shekara 18 da 19 suka fadi tare da amaryar da 'yar uwar angon.

Angon ya ceto 'yar uwarsa ta hanyar jan ta daga cikin ruwan amma sauran sun bace a karkashin ruwan. 'Yan sanda sun ce an gano gawarwakin kuma za a yi bincike a kansu.

Wannan dai shi ne bala'i na baya-bayan nan da ya danganci daukar hoton 'selfie' a Indiya.

Kwararru sun yi gargadin cewa mutane na jefa kansu cikin hadari na babu gaira babu dalili don su birge abokai da 'yan uwansu a shafukan sada zumunta.

A jihar Haryana a watan Mayu, wasu matasa uku da ke daukar hoton 'selfie' a kan titin jirgi sun mutu bayan da suka kauce wa wani jirgi da ke tunkaro su, amma suka fada wa wani jirgin da ya taho ta bayansu.

A shekarar 2017, jihar Karnataka a Indiya ta kaddamar da wani kamfe don gargadin mutane kan cewa "selfie na kisa" bayan mutuwar daliban hudu.

A shekarar ne kuma wani mutum ya mutu a Odisha lokacin da yake daukar 'selfie' da wata giwa, ta nade shi da hancinta sannan ta matse shi har sai da ya mutu.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment