Tuesday, 8 October 2019

Rahoto kan yadda shugaba Buhari ya mika kasafin kudin 2020 ga majalisa

Wasu 'yan majalisa sun kaure da kiran 'Sai Baba' lokacin da Shugaba Buhari ya isa zauren majalisar wakilan kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabin gabatar da daftarin kasafin kudin 2020, inda da farko ya fara yaba wa majalisar dokokin kasar bisa kokarinsu na aiki tare da bangaren zartarwa.


Shugaba Buhari ya ce daftarin kasafin kudin zai kara harajin kaya daga kaso 5 cikin 100 zuwa 7.5 cikin 100.

Ya ce za a yi amfani da harajin ne wurin inganta fannin kiwon lafiya da ilimi da gine-ginen hanyoyi.

Shugaba Buhari ya ce an gina kasafin kudin ne a kan dala 57 na farashin gangar danyen mai.


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an samu karin kaso 9.75 cikin 100 a kan kasafin kudin shekarar 2019 na kusan naira tiriliyan 9.

Hakan na nufin kasafin kudin Najeriya zai kama fiye da naira tiriliyan 10.

Shugaba Buhari ya kammala jawabi inda ya mika kundin daftarin kasafin kudin na 2020 ga majalisar dokokin Najeriya.
BBChausa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment