Wednesday, 9 October 2019

Ruwanda ta kafa kamfanin samar da wayar hannu na farko a Afirka

A karon farko a nahiyar Afirka gwamnatin Ruwanda karkashin Shugaba Paul Kagame ta jagoranci kafa kamfanin samar da wayar hannu.


A ranar Litinin din nan aka yi bukin kaddamar da kamfanin mai suna "Mara da zai dinga samar da wayar hannu dake da Android a Kigali Babban Birnin Kasar.

Akwai kusan mutane 200 da za su yi aiki a kamfanin inda farashin wayoyin hannun da za su samar zai fara daga dala 129 zuwa 189.

A jawabin da Shugaban Kasar Ruwanda Paul Kagame ya yi a wajen ya fadi cewar za a iya sayen wayoyin ta hanyar biya a hankali a cikin shekaru 2 kuma ba wai ana sayen wayoyin hannu ne ba ne don burgewa ko nuna isa a sai don biyan bukatar yau da kullum kuma cikin hanzari.

Babban jami'in kamfanin Marsa mai suna Ashish Thakkar ya ce ba wai jojjona sassan wayar kawai za a yi a Ruwanda har ma da samar da dukkan kayan ta a kasar wanda wannan wani babban mafarkin nahiyar Afirka ne.

A Ruwanda dake son fitar da wayoyin zuwa kasashen Afirka kaso 52 na jama'a na samun yanar gizo.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment