Sunday, 13 October 2019

Sarkin Kano ya sallami bafadenshi daga aiki bayan shiga tawagar tarbar gwamna Ganduje

Rahotanni daga jihar Kano na cewa me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya kori daga daga cikin fadawashi, Maja Siddin Sarkin Kano, Alhaji Auwalu daga aiki bayan da ya shiga cikin wanda suka wa gwamna Ganduje tarbar dawowa daga tafiya da kuma murnar yin nasara a kotun sauraren karar zabe.Lamarin tarbar da akawa Ganduje an yi shine lokacin Sarki Sanusi baya gari amma da ya ji labarin Alhaji Auwalu ya shiga cikin wanda suka yiwa gwamna tarba abin ya bata mai rai.

Wani abu daya kara saka saka Alhaji Auwalu wanda aikinshi shine shiryawa Sarki dokin da zai hau shine daga hoton tsohon sarkin Kano, Marigayi Alhaji Ado Bayero da yati a wajan tarbar.

An kori Alhaji Auwalu daga aiki sannan kuma ya fita daga gidan da yake zaune a ciki fiye da shekaru 30 da suka gabata, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

Wasu mazauna fadar da basu bayyana sunayensu ba sun nuna rashin jin dadin korar Alhaji Auwalu inda suke ganin hukuncin da aka mai yayi tsari. Bafaden sanannene a cikin fadar Kano.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment