Wednesday, 9 October 2019

Sharhi Akan Zancen Lalata Da Yara Mata A Jami'o'i

Abunda zan rubuta yanzu da yawa cikin Malaman jami'ah sun san haka yake, amma galibi kowa zai kauda kai ne saboda gudun zargi, ko kuma kar ace yana baiwa cutar da dalibai kariya. Duk da yiwuwar hakan, ba zai hanani bayyana abunda na sani ba, saboda shi ma wani ilimi ne da boye shi ya kan iya zama nau'in zalumci.


Ina son mutane su gane cewa a ka'idar jami'ah; ba laifi ba ne Malami yayi soyayya da dalibar shi mace. Malamai da dama sun yi soyayya da daliban su mata har sun yi aure har da y'ay'a. Ko a jami'ar da nake aiki an yi irin wannan aure da dama kuma Allah ya albarkace su da zurri'ah.

Ita Jami'ah babban wajibine gareta ta kare hakkin dalibai da Malamai daga cin zarafi kowanne iri ne, saboda haka tilas ne hukumar Jamiah ta tabbatar da cewa ba tilas ko barazana aka yi wa daliba ko dalibi ba. Idan ko babu tilas cikin abunda ya faru; shikenan magana ta zama zabin mutane biyu masu hankali.

Bisa shekarun da na yi ina aiki a jami'ah na san cewa ba lallai ne irin wannan halayya ta nema tsakanin Malami da daliba ya zama laifin Malamai kadai ba. Su ma dalibai mata suna taka rawa mai yawa wajen gabatar da kawunan su wajen Malaman na su. Hakanan kuma yadda dalibar kan iya yarda da Malamin shi ma Malamin kan iya yarda da dalibar.

Sannan wannan video ya nuna cewa dalibar ta kai kan ta ne da niyyar Jan hankalin Malamin, sannan ta yi sintiri wajen shi har sau uku, duk abunda ya fada tana amincewa da shi, ina gani ko Sarkin gari ne za'a iya kamawa a wannan yanayi ba Malami kadai ba. To ta yaya wannan video zai zama cikakkiyar hujja akan Malamin? Sai dai a kama shi da laifin "abusing office" amma sexual harassment kam ina gani yarinyar ce ta bashi kofa, kamar yadda dama mun San cewa manufar ta kenan.

Saboda haka ina bada shawarar cewa yadda aka samu yan jarida suka yi kyakkyawan bincike akan yadda wasu Malaman jamiah ke amfani da damar su wajen bata yara mata, akwai bukatar irin wannan bincike wajen gano shin dalibai matan ma kan iya haddasa irin wannan halayya?
Daga Sheriff Almuhajir PhDKu biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment