Friday, 4 October 2019

'Yadda ake auren mut'ah da kananan yara a Iraki': Labari me sosa Zuciya

Wani binciken kwakwaf da BBC ta yi kan auren mut'ah ta gano yadda wasu malamai ke gudanar da auren mut'ah da kananan yara a Iraki.


Binciken sirrin da BBC ta yi a daya daga cikin wuraren da malaman suke domin gudanar da irin wannan aure ta gano cewa malaman na daura auren mutu'a na takaitaccen lokaci, a wani lokacin ma har na zuwa sa'a daya ko kwana daya.

Wasu malaman ma na aurar da har mata 'yan shekara tara domin a sadu da su.

Binciken ya gano cewa malaman na sa albarka ga yara wadanda ba su kai shekarun aure ba domin su zama amare na takaitaccen lokaci.
Auren Mut'ah
Auren mut'ah wani sashe ne na addini a mazhabar Shi'a da wasu daga ciki ke yi, inda ake aure na dan takaitaccen lokaci, ana kuma biyan matan da aka yi auren da su kudi kafin gudanar da auren.

Asali auren mut'ah ana yin shi ne idan mutum zai yi tafiya sai ya tafi da matar, amma a yanzu namiji da mace za su yi auren mut'ah su zauna a gari daya na dan wani lokaci.

Auren mut'ah ya rarraba kan malaman musulunci inda wasu na daukarsa a matsayin karuwanci wasu kuma na ganin ya hallarta, kuma ana muhawara kan tsawon da za a iya dauka na zaman auren.

Sashen larabci na BBC a Iraki ya yi bincike na watanni 11, inda BBC ta yi shigar burtu, inda wakilanta suka rinka zuwa wurin malaman domin nemo irin wadannan matan don cinikin auren mut'ah da su.

A lokacin da ake wannan ciniki, duk BBC na daukar abubuwan da ke faruwa a bidiyo cikin sirri .

BBC ta tattauna da matan da aka yi auren mut'ah da su da kuma wasu daga cikin mazan wadanda suka biya malaman domin nemo masu matan da za su yi auren mut'ar da su.

Bayan an shafe kusan shekaru 15 ana gwabza yaki a Iraki, an yi kiyasin cewa kusan mata miliyan daya mazansu sun mutu wasu kuma matan sun rasa muhallansu.

BBC ta gano cewa akwai mata da yawa da suna yin auren mut'ah ne sakamakon talauci.


Wuraren da ake yin auren Mut'ah a Iraki

Binciken da BBC ta yi ya gano cewa ana yin wannan auren a manyan masallatan Shi'a guda biyu a Iraki.

Misali, masu binciken sun samu malamai 10 a Khadhimiya da ke Bagadaza. Takwas daga cikinsu sun bayyana cewa za su gudanar da auren mut'ah; rabinsu sun yarda za su daura auren da 'yan shekara 12 zuwa 13.

Masu binciken na BBC sun kuma hadu da wasu malaman a Karbala, wanda shi ne wuri mafi girma ga 'yan Shi'a a duniya, biyu daga cikin malaman sun yarda za su hada auren mut'ah da yara mata kanana.

BBC ta nadi bidiyon wasu malamai guda hudu a cikin sirri, uku daga cikinsu sun ce za su samar da mata balagaggu domin auren mut'ah, biyu kuma sun ce za su samo kananan 'yan mata.

Sayyid Raad, wani malami a birnin Bagadaza ya shaida wa wakilin BBC mai binciken kwakwaf cewa shari'a ba ta kayyade takamaiman shekarun auren mut'ah ba: ''Namiji zai iya auren ko mata nawa yake so, za ka iya auren mace ko da na minti talatin, idan lokaci ya yi shi kenan, za ka iya auren wata ma nan take.

Auran masu shekaru tara


A lokacin da BBC ta tambayi Sayyid Raad idan shari'a ta yarda da yin auran mut'ah da karamar yarinya sai ya ce, 'a bi a hankali kawai kada ta rasa budurcinta.''

Ya kara da cewa "Za ka iya yin wasa da ita, ku dan kishingida, ka taba jikinta da mamanta... Ba za ka sadu da ita ba ta gaba. Amma zuwa mata ta dubura ba matsala." Da aka tambaye shi me zai faru idan yarinyar ta ji zafi, sai malamin ya ba da amsa cikin kaduwa. "Wannan tsakaninka da ita ne, kuma shin za ta iya jure radadin ko kuwa."

An tambayi Sheki Salawai, wani babban malami da ke Karbala idan za a iya auren mut'ah da 'yar shekara 12 inda ya ce ''Eh babu matsala da 'yar shekara tara - babu matsala kwata-kwata. shari'a ta yadda.''

Auren Mut'ah ta waya


Domin tabbatar da wannan batu na auren mut'ah da kananan yara, mai binciken ya kirkiri sunan wata yarinya mai suna ''Shaimaa'' inda ya shaida wa Sheik Sayyid Raad cewa yana so ya yi auren mut'ah da ita.

A gaske, wakilin BBC ya yi wasa da hankalin yarinyar ta wayar tarho.

Sayyid Raad bai nemi ya hadu da yarinyar ko ya yi magana da iyayenta ba, kai tsaye sai ya amince wa wakilin BBC cewa zai daura auren ta waya. Sun yi wannan alkwarin ne zaune a cikin mota tasi tare da wakilin na BBC.

Suna zaune sai ya kira yarinyar ta waya ya tambaye ta: ''Shaima kin amince za ki aure shi tsawon kwana daya kan dinari dubu 150?''A karshe sai ya ce. ''Yanzu kun zama ma'aurata kuma za ku yi zama na halal tare.''

Sheik Sayyid ya bukaci a biya shi dala 200 na 'yan mintunan da ya yi wajen daura auren, inda daga karshe wakilin BBC ya biya wadannan kudade.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment