Friday, 4 October 2019

Yadda Wasu Hausawa Kiristoci Suka Hana Mu Shiga Wani Kauye A Kano Domin Yin Da'awa

WANI ABIN TAKAICI DA YA SAME MU

A ranar Lahadi 29-09-2019 mu ka shirya fita Da'awar addinin musulunci zuwa wani gari da ake kira "Faala" a cikin karamar hukumar Tudun Wada a Jihar Kano Arewacin Nigeria, inda daga nan kuma zamu gangara mu shiga wani Lungu da ake kira da "Bangaa" a dai Karamar Hukumar Tudun Wada Jihar Kano domin dubiyar wani Musulmi maras lafiya da ke cikin wannan Kauye na "Bangaa". Da kuma isar da sakon musulunci idan dama ta samu.


Garin Faala karamin kauye ne dake dauke da al'umma sama da dubu, kuma dukkan su Musulmi ne babu Kirista ko Bamaguje ko Mutum daya. Har ma suna da Katon masallacin Juma'a.

Tafiyar Mintuna talatin (30) ne ko kusa da haka a tsakanin garin Faala da kuma wani karamin Kauye mai suna "Bangaa" wanda ke karkashin dagacin Faala.

Shi wannan karamin kauye mai suna "Bangaa" baki dayan garin Kiristoci ne, in banda Mutum biyu (2) ko uku (3)

Bayan mun isa garin Faala a yau Lahadi 29- Sept. 2019,mun shiga fadar Mai girma Dagacin garin mun yi gaisuwa a gare shi ta ban girma, mun kuma sake neman izini a gare shi, duk da cewa mun aika masa sakon zuwan mu da kuma neman izinin gabatar da wa'azin musulunci a yankinsa. Kuma ya amince ya bamu goyon baya kamar dai yadda doka ta tanada.

Bayan mun gaisa da Mai girma dagaci, mun nemi ya hada mu da wakili wanda zai yi mana jagora domin shiga kauyen Bangaa, kauyen da baki dayansa kiristoci ne in banda mutum biyu ko uku da suke musulmai, inda Dagaci ya hada mu da da'nsa na cikinsa wanda shima yana da sarautar mai unguwa,Mai Unguwa yayi mana jagora muka hau mota tare dashi domin isa zuwa ga kauyen Bangaa, muyi dubiyar maras lafiya,sannan muyi amfani da dama idan ta samu muyi kira zuwa ga addinin Islam.

Mun kama hanya mun durfafi kauyen Bangaa, wanda da kyar mota ke iya shiga saboda ramuka da kwazazzabai da ciyayi da itatuwa, kwatsam!!! Bayan mun yi tafiya ta kimanin mintuna ashirin a cikin jeji, muna daf da shiga kauyen!!! Sai ga dandazon matasa majiya karfi kimanin mutum (7) sun tare hanya sun gindaya baburansu.

A nan Matasan nan suka tsayar da mu, suka ce bamu isa mun shiga kauyen su ba. Idan kuma muka shiga to sai dai iyayen mu su haifi wasu. Suna zagin mu, suna yi mana barazana iri-iri, mu kuma muna lallashin su da basu hakuri, inda a karshe duba da wasu dalilai na maslaha da gudun fitina muna ji muna gani muka hakura muka juyo cikin rashin jin dadi.

Matasan sun fito ne daga kauyen bisa umarnin Shugaban su (Pastor) wanda asalinsa dan jihar Katsina ne,ba ma Dan Jihar Kano bane!!! Kawai Kungiyar kiristoci ce ta dauko shi ta kawo shi wannan kungurmin lungun domin yana jagorantar cocinsu.

Ko a waccan shekarar mutanen mu sun shiga garin Bangaa da nufin su gaisawa da shi don su fahimci juna, amma suna shiga yasa aka debo makamai aka koro su.

To yau ma sai ga shi ya sake bayar da umarni, yace mabiyansa kada su sake su bari mu shiga masa gari. (Kai kaji rashin kunya da raini wai garinsa, alhali akwai mai unguwa akwai dagaci da ke da iko da kauyen)

Haka nan shi Mai Unguwa da aka hada mu dashi a idonsa komai ya faru, yayi ta kokarin basu baki, yayi magiya, yayi lallashin, amma suna dukan kirjinsa suna zage-zage da ashariya suna nuna mu da yatsu cewa mu janye motocin mu, kada mu sake mu shigar musu kauye!!! Sun bamu dan lokaci mu bar wajen ma da suka dakatar da mu ko kuma duk abinda suka yi mana ba ruwansu!!!

Mai Unguwa dai ya sake bamu labari cewa, shi wannan Pastor shugaban cocin kauyen Baaga wanda Mutumin Katsina ne, kwanaki yazo har cikin gidan Dagaci yana masa kashedi da cewa ya daina bari musulmi suna shiga masa gari fa!!!.

Yan uwa masu karatu wannan fa dambarwa ta faru ne a cikin Jihar Kano ba a Enugu, ko Onitsha, ko wani gari cikin manyan garuruwan kiristoci a Nigeria ba!! A'a a jihar Kano!!!

Wanda mun san a tsarin dokar kasa babu wani farar hula da ya isa ya hana wasu shiga wani waje, babu wanda ya ke da ikon hana wasu yin kira zuwa ga kowanne addini.

Amma sai gashi abun takaici Pastor ya hana Musulmi Yan cikin Jihar Kano, kuma har ma da Yan karamar hukumar, kai har ma da mai sarautar gargajiya shiga wani kauye domin suyi dubiyar maras lafiya su kuma yi da'awar addininsu.

Hakika wannan raini ne!!! Wannan cikin kashi ne!!! Wannan sakaci ne na musulman Jihar Kano da har muka bari aka shigo aka raina mu haka.

(1) Mun sanar da wannan abu ne da ya faru domin mu janyo hankulan Y'an uwan mu Musulmi, su sani cewa muna gidajen mu muna sharar bacci kiristoci suna aiki ba dare ba rana, sunyi amfani da damammakinsu sun shiga kauyuka da lunguna sun yi karfi sun kuma cusa kiyayya a zukatan mutanen kauyen akan Yan uwan su a harshe da al'ada da jinsi.

(2) Wajibi ne zamu dauki matakin da ya dace na shari'a bisa yadda doka ta tanada akan wannan Pastor da yayi mana barazana ya kuma tauye mana hakkokin mu.

(3) Muna kira ga dukkan al'ummar musulmin Jihar Kano da ma kewaye, su sani akwai aiki a gaban mu matuka. Wallahi idan ka shiga lungunan wasu kananan hukumomin Kano,kamar: 

Tudun Wada,Sumaila,Garko da makamantansu zaka sha mamaki na irin barnar da kiristoci su kayi a wadannan wurare! Domin yau Lahadi mun ga abubuwan takaici a kan hanyar mu. Saboda haka ya zama wajibi mu farka daga baccin da mu ke yi! Mu tashi da gaske mu taimaki wannan addini namu na gaskiya.
Allah Ya sauwaka Allah Ya sa mu dace.
Mai rubutu:
Musa Muhammad Idris Dankwano.
29-08-2019.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment