Thursday, 3 October 2019

Yaga Sakamakon Zaben Gama, Kotu Ta Wanke Gawuna Da Garo

Sabanin abin da jama'a suka sanu kuma suka gaskata a kan sakamakon zaben gama, Jastis Halima Shamaki, babbar alkaliyar kotun sauraron korafin zaben gwamna a jihar Kano, ta fadi abin da ya girgiza Kana wa a kan yaga sakamakon zaben.


Abin da Jastis Shamaki ta fada ya wanke Gawuna da Sulen-Garo daga zargin da ake yi musu na yaga sakamakon zaben mazabar Gama, lamarin da yasa har jami'an 'yan sanda suka kama su a daren ranar 10 ga watan Maris.

"Takardun sakamakon zaben da masu korafi suka gabatar basu da hatimin hukuma, kuma babu saka hannu. Wasu kuma an yi rubutu a jikinsu, a saboda haka batun yaga sakamakon zabe ya zama jita-jita da kotu ba zata karba ba.

"Dakta Yakasai ya samu damar sauya sakamakon zaben da aka sace bayan ya rufe kansa a dakin da sakamakon zabe yake," a cewar ta.
Sarauniya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment