Saturday, 12 October 2019

'Yan bindiga sun kashe mutum 16 a masallaci

Wasu masu ikirarin jihadi sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Salmossi na kasar Burkina Faso yayin da mutane ke tsaka da sallah a ranar Juma'a.


Mutum 16 ne suka mutu a harin, inda suka tilasta wasu da yawa tserewa daga kauyen da ke Oudalan kusa da kan iyakar kasar da Mali.

Mutum kusan 1,000 ne da suka fusata suka hau kan tituna a babban birnin kasar Ouagadougou domin nuna bacin ransu tare da yin Allah-wadai da kasancewar sojojin kasashen waje a yankin.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce sama da mutum 200,000 ne suka tsere daga muhallansu a Burkina Faso a cikin wata uku da suka wuce.

A makon da ya gabata ma 'yan bindiga sun kashe mutum 20 a wata mahakar gwal a yankin Soum mai makobtaka.

Hukumomin bayar da agaji na ci gaba gargadi kan karuwar hare-hare da kuma halin ni-'yasu da jama'a ke ciki a yankin.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment