Friday, 11 October 2019

'Yan matan Arewa ne koma baya a Najeriya'

Wata mai fafutukar kare hakkin mata a Najeriya, Dakta Mairo Mandara ta bayyana yankin arewa a matsayin wanda yake fuskantar koma baya ta fuskar sa yara mata a makaranta inda ta ce akwai 'yan mata miliyan 14 da ya kamata a ce suna makaranta amma ba sa zuwa.


Dakta Mandara ta bayyana hakan a hirar da ta yi da BBC a wani bangare na tattakin da wasu kungiyoyi suka shirya gudanarwa a ranar Juma'a dangane da ranar tunawa da 'ya'ya mata ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara gudanarwa a kowace ranar 11 ga watan Oktoba.

Taken ranar na bana shi ne "Rundunar mata: Ba a fada muku, Ba a kwabarku."

A cewarta, sun shirya tattakin domin jawo hankalin gwamnati ta tabbatar cewa 'duk 'ya mace a Najeriya ta samu ilimin sakandare kyauta sannan a rika koya wa yara mata sana'o'i a makarantun saboda su dogara da kansu ko da ba su samu damar ci gaba da makaranta ba.
Ta kara da cewa 'ya kamata gwamnati ta sa makarantar 'ya mace ta zama kyauta ga 'ya'yan masu kudi da na marassa karfi kuma ya zama tilas kowace 'ya mace ta gama sakandare a kasar domin ta san hagu da dama ta kuma iya karatu da rubutu.

Likitar ta kuma ce rashin sa yara mata a makaranta na jefa rayuwarsu cikin hadari ta yadda suke fuskantar barazanar gurbatar tarbiyya.

A cewar mai fafutukar, jihohin Borno da Yobe da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sokoto da kuma Kano su ne jihohin da ke gaba-gaba a rashin sanya yara mata a makaranta.

Dakta Mairo Mandara ta bukaci iyaye da su mayar da hankali wajen ba wa 'ya'ya mata ilimi saboda mahimmancinsa ta yadda da ilimin ne, a cewarta, yara matan za su samu damar tallafa wa 'yan uwansu da iyayensu har ma da al'umma baki daya.

Ita kuwa shugabar wata kungiyar mata matasa a Ghana mai taken Young Women Leaders Network, Hajjo Dikko Usman ta ce matsalolin da yara mata suke fuskanta a kasar sune auren wuri da rashin ilimi mai zurfi da rashin kiwon lafiya saboda karancin asibitoci a matakin farko.

A cewarta, matukar ana son a sauya wannan al'amari, dole ne a ilmantar da 'ya'ya mata da iyayensu su san amfanin karatun da koyar da su sana'o'in hannu da za su taimaka musu wajen dogaro da kansu.


Sai dai a Jamhuriyar Nijar, wata matashiya mai suna Sharifa wadda yanzu haka take zaune a gida ba tare da zuwa makaranta ba, saboda iyayenta ba su da halin biya mata kudin jarrabawa ta shaida wa BBC cewa tana son ta ga ta yi karatun likita amma rashin kudi ya sa burinta bai cika ba.

Ta ce ba ta jin dadi kuma har kuka take yi idan ta ga sa'o'inta suna zuwa makaranta yayin da ita kuma take zaman gida.

Wasu alkaluma na cewa akwai 'yan mata miliyan 130 a fadin duniya da har yanzu ba sa zuwa makaranta.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment