Wednesday, 9 October 2019

Yawan Haihuwa yana kawo Sankarar Mahaifa>>Inji Matar Gwamna

Masu bincike sun ce cutar cancer ko sankarar mahaifa ta fi tsanani a arewacin Najeriya saboda yawan haihuwa, a cewar matar gwamnan jihar Kebbi a Najeriya.


Duk da karancin cibiyoyin kula da masu cutar kansa a Najeriya, wasu alalumman binciken sun nuna cewa yawan masu kamuwa da cutar a ƙasar na ƙaruwa ne duk shekara, wanda ya kasance wata babbar barazana musamman ma ga mata.

Dr Zainab Shinkafi Bagudu, shugabar gidauniyar MedicAid da ke bincike da kiɗayar masu fama da cutar a Najeriya da kuma bayar da tallafi, ta shaida wa BBC cewa kansar mahaifa ta fi shafar mata a arewaci, yayin da kuma kansar mama ta fi addabar mata a kudancin Najeriya.Ta ce bincikensu ya nuna sama da mutum dubu ɗari biyu da hamsim ke kamuwa da cutar kansa a Najeriya duk shekara.

Ta yi kira ga mata a arewacin ƙasar su rungumi tsarin taƙaita haihuwa a matsayin rigakafi.

"Yawan haihuwa ke ƙara kawo cutar kansa, ya kamata a tsara iyali a samu hutu," in ji Dr Bagudu wadda ƙwararriyar likita ce a fannin kula da lafiyar yara musamman jarirai bakwaini waɗanda ba su isa haihuwa ba.

Kansa dai cuta ce da ke da wuyar sha'ani da kuma tsadar magani, kuma Dr Zainab ta ce rudanin da ke tattare da cutar kansa ne ya ja hankalinta ga kafa gidauniyar yaki da cutar.

A ranar 26 ga watan Oktoba za ta jagoranci tattaki na mutum miliyan ɗaya a Abuja game da cutar kansa wanda gidauniyar da ta kafa sama da shekaru 12 ke gudanarwa duk shekara.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment