Thursday, 28 November 2019

A karin farko Madrid ta yi wasa me kyau tun bayan tafiyar Ronaldo

A karin farko tun bayan tafiyar Cristiano Robaldo, kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yi wasa me kyau da daukar hankali Kamar dan wasan yana nan.Hakan ya farune a wasan da Madrid a buga da PSG na gasar cin kofin Champions League Ranar Talatar data gabata.

Madrid tq rufa PSG da kai hare-hare inda ta kai jimular hari 27 a wasannan sannan aka samu guda 12 daga ciki wanda suka yi kyau.

Tsohon golan Madrid Navas da a yanzu yake a PSG yayi kokari sosai wajan tare da yawa daga cikin kwallayen in banda haka da Madrid ta tarawa PSG kwallaye na ban mamaki a wasan.

Hazard shi ma yq dauki hankula sosai saidai daga baya an cireshi daga wasan bayan aunin da ya samu amma an tabbatar da cewa raunin nashi ba me tsanani bane kuma zai dauki kwanaki 10 ne kawai yana jinya.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment