Thursday, 28 November 2019

Afrika ta Kudu ta samar da maganin Kanjamau

Afrika ta Kudu ta ce, za ta kaddamar da maganin Kanjamau na zamani kuma mai rahusa domin yaki da cutar a tsakanin dimbin al’ummar kasar da ke fama da ita.

An samar da maganin mai dauke da nau’ukan sinadarai uku tare da tallafin Kungiyar Bunkasa Kiwon Lafiya ta Duniya.

Daga cikin sinadaran har da Dolutegravir wanda Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a matsayin sinadarin maganin da ke kan gaba wajen yaki da cutar.

Darektan Kungiyar Bunkasa Lafiyar ta Duniya, Robert Matiru ya ce, sabon maganin na TLD na da tasiri matuka, kuma yana murkushe kwayoyin cutar cikin gaggawa fiye da maganin da ake amfani da shi a yanzu haka.

Afrika ta Kudu dai, nada sama da kashi 10 daga cikin jumullar alkaluman mutane da ke mutuwa a sanadiyar cutar HIV, yayin da kuma take da kashi 15 na jumullar sabbin mutanen da ke kamuwa da ita .
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment