Thursday, 7 November 2019

An dakatar da Tauraron dan kwallon Najeriya bayan da ya dallawa Rafali Mari

Hukumar kwallon kafa ta jihar Nasarawa ta hukunta wani dan kwallon jihar me suna Yakubu Hassan dake bugawa kungiyar kwallon kafa ta Duba Gari a jihar wasa bayan cun zarafin alkalin wasa da yayi.Yakubu ya fallawa alkalin wasa, Kassim Adamu mari ne yayin da suke buga wasa da wata kungiya me sun Winda a ranar 29 ga watan October da ya gabata.

Hukumar kwallon kafa ta jihar ta bayyana cewa ta dakatar da Hassan har sai mama ta gani sannan kuma an ci kungiyar tashi tara.

Kungiyar alkalan wasa na jihar Nasarawa ta bayyana cewa daga yanzu duk wasan da aka kara saka Hassan zata bijire mai.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment