Sunday, 3 November 2019

An Fara Kai Manyan Kayayyaki Wurin Da Ake Hako Man Fetur A Jihar Bauchi

Biyo bayan samun man fetur da iskar gas da akai a rijiyar Kolmoni II dake yankin Barambu a karamar Hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, yanzu haka murna ta mamaye yankin, yayin da al'ummar yankin suka wayi gari da ganin ma'aikatar NNPC ta fara tura manyan Injinan man fetur yankin.


Daya daga cikin mazauna yankin, mai suna Alhassan Abbas Musa, dan shekaru 55 ya bayyana cewa, ba za su iya bayyana farin cikin da suke a fili ba, sai da a ganshi a fuskar su, ya kuma kara da cewa, su kan sun ba baya, amma suna fatan wannan Arziki ya amfani 'yan bayan su.

Ya kara da cewa yana fatan wannan man fetur ya amfani al'ummar Arewa, da ma Nijeriya da 'yan baya masu taso wa baki daya.

Malam Alhassan ya yaba wa shugabancin shugaba Buhari ganin yadda yayi tsayin daka wajen tabbatar da hako wannan Man Fetur a Arewacin Nijeriya, ba kamar yadda Gwamnatocin baya suka yi ta shure wannan abin alkairi ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment