Sunday, 10 November 2019

An Kwace Masallaci an baiwa Mabiya Addinin Hindu a India

Kotun kolin Indiya ta ce a mika wurin bauta na Ayodhya wanda ake ta takaddama a kai ga mabiya addinin Hindu, wadanda ke son yin amfani da shi domin gina nasu wurin bautar.


Kotun ta yanke wannan hukunci ne domin kawo karshen takaddamar da aka kwashe gomman shekaru ana tafkawa tsakanin Musulmai da mabiya addinin Hindu, a kan wanda ke da hakkin mallakar wurin mai tarihi a jihar Utter Pradesh.

Kotun ta ce a bai wa Musulmai wani filin da za su gina nasu masallacin.


Mabiya addinin Hindu sun yi amannar cewa a wurin ne aka haifi daya daga cikin ababen bautarsu mafiya tsarki.


Su kuma Muslumai na ikirarin cewa sun kasance suna ibada a wurin shekara da shekaru.

Takaddamar ta kara zafi ne a shekarar 1992, bayan da wasu matasa mabiya addinin Hindu suka rusa wani masallaci mai tarihi da ke wurin, wanda aka gina a karni na 16.

Me kotu ta ce?

A hukuncin da ta zartar, wanda daukacin alkalanta suka amince da shi, kotun ta ce rahoton Hukumar Safiyo ta Indiya ya nuna cewa an gano burbushin wani gini da ke karkashin ginin masallacin na Babri da aka rusa, wanda asalin sa ba gini ne na Musulmai ba.

Kotun ta ce bayan la'akari da hujjojin da aka gabatar mata, ta yanke hukuncin cewa a mika filin da ake rigima a kansa ga mabiya addinin Hindu domin su gina wurin bauta, su kuma Musulmai a ba su wani filin na daban inda za su gina masallaci.

Daga nan kuma sai kotun ta umurci gwamnatin kasar da ta kafa wata gidauniya da za ta lura da ginin wurin bautar.

Sai dai duk da haka kotun ta ce rushe "Masallacin Babri" da mabiya addinin Hindu suka yi ya saba wa doka.


Mene ne martanin al'umma?

Duk da umurnin da hukumomi suka bayar na cewa kada a yi bukukuwa bayan yanke hukunci, wakilin BBC da ya je kotun ya ce ya ji ana sowa ana furta kalamai na godiya ga abin bautar mabiya addinin Hindu, inda ake cewa "Jai Shree Ram".

Wani lauyan mabiya addinin na Hindu ya ce "An yi adalci a wannan hukunci, kuma al'ummar Indiya sun yi galaba."

Sai dai masu wakiltar Musulmai a kotun sun ce ba su gamsu da hukuncin ba, kuma suna tunanin mika bukatar a sake bibiyar hukuncin bayan sun gama nazari a kansa.

An dai jibge dubban 'yan sanda a birnin, yayin da kantuna da makarantu za su kasance a kulle har zuwa ranar Litinin.

Daruruwan mutane ne aka damke a yankin a ranar Juma'a gabanin yanke hukuncin saboda tsoron tashin hankali.
BBChausa.


Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment