Wednesday, 6 November 2019

An nuna wa Osinbajo wariya a gwamnatin Buhari>>Kungiyar kare muradun yarbawa

Wasu ƙungiyoyi a Najeriya sun yi zargin cewa ana mayar da mataimakin shugaban ƙasar Farfesa Yemi Osinbajo ɗan kallo a tafiyar da al'amuran ƙasa.


Ƙungiyoyin waɗanda suka haɗa har da ta Yarbawa ta Afenifere sun yi wannan zargi ne biyo bayan ɗaukar dokar hana haƙar mai da shugaban ma'aikata Abba Kyari ya yi har Landan don kai wa Shugaba Muhammadu Buhariya ya sanya mata hannu.

Suna kallon hakan a matsayin ƙoƙarin mayar da Farfesa Osinbajo saniyar ware da ƙin miƙa masa ragamar mulki, al'amarin da ya jawo ce-ce ku ce. Sai dai tuni ɓangaren shugaban ƙasar ya musanta zargin.
Ƙungiyar Afenifere ta shaida wa jaridar Punch ta kudancin ƙasar cewa "in dai har sai shugaban ma'aikatar fadar shugaban ƙasa ya ɗauki takardu takanas ya tafi har Landan ya kai wa shugaban ƙasa ya sanya musu hannu, to hakan na nufin an fitar da Osinbajo daga hidimar gwamnati kenan."

Wani lauya, Barista Al Zubair Abubakar ya ce Shugaba Buhari bai saba doka ba da ya sa hannu kan sabuwar dokar hakar man da majalisar dokokin ƙasar ta amince da ita yayin da yake bulaguro a Burtaniya.

Barista Abubakar ya bayyana hakan bisa dogaro da kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bai wa shugaban ƙasa dama idan zai yi tafiya, tafiyar da ta wuce kwana 21 yana da damar ya bayar da ragamar mulki ga mataimakinsa ta hanyar sanar da majalisar ƙasa.

Tun bayan da Shugaba Buhari ya sanya wa dokar hannu ne dai, jama'ar ƙasar ke ta mayar da martani inda wasu ke cewa shugaban kasar bai yi dai-dai ba saboda a cewarsu, kamata ya yi a ce mataimakinsa Yemi Osinbajo ne zai sanya hannu a kan dokar tun da shi Buharin yana Burtaniya.

A ƙarin hasken da lauyan ya yi ya ce ''tafiyar da Buhari ya yi ya bar Saudiyya, zai dawo Najeriya ranar 20 ga wannan wata, abinda ke nuna cewa bai kai kwana 21 ba kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ce.''


Ya ƙara da cewa ''tafiyar da ya yi ba ta rashin lafiya ba ce, tafiya ce ta hutu kuma hakan bai hana shi aiki ba'' wanda a cewarsa, ''yana aiki ne a matsayinsa na shugaba daga inda yake.''

Lauyan ya kuma ce Buhari ''shi ne shugaban ƙasa na farko tun shekarar 1999 da ya bayar da ragamar mulki ga mataimakinsa a yayin da ba ya ƙasar.''

A baya-bayan nan ma, Shugaba Buhari ya kaddamar da majalisar ba shi shawara kan tattalin arziƙi bayan rushe kwamitin tattalin arziƙin ƙasar da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta, al'amarin da shi ma ya jawo ce-ce ku cen.

Yayin da wasu ke cewa son barka, wasu dai na kallon matakin a matsayin yunƙurin rage ikon mataimakin shugaban kasar, zargin da fadar gwamnatin ta bakin mai magana da yawunta, Garba Shehu ta musanta.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment