Friday, 8 November 2019

An sace man fetur na Dala biliyan 38 a Najeriya

Hukumar Kula da Arzikin Karkashin Kasar da ake hakowa a Najeriya ta ce, kasar ta yi asarar man fetur da barayi suka sace da kudinsu ya zarce Dala biliyan 38 da rabi a cikin shekaru 10.


Alkaluman da hukumar ta bayar sun nuna cewar, daga cikin wannan adadi, an sace danyan man da ya kai na Dala biliyan 1 da rabi a cikin gida, da kuma tacaccen mai na kusan Dala biliyan 2 daga shekarar 2009 zuwa 2018.

Hukumar ta ce wadannan sace-sace na daga cikin matsalolin da suka shafi kudaden shigar da Najeriya ke samu, wanda ya nuna cewar a kowacce rana kawai ana sace man da ya kai na Dala miliyan 11, wato Dala miliyan 349 kenan a kowanne wata.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment