Wednesday, 6 November 2019

An tube Xhaka Kaftin na Arsenal an ba Aubameyang

Kocin Arsenal Unai Emery ya tube Granit Xhaka a matsayin kaftin inda ya nada Pierre-Emerick Aubameyang


Matakin tube Xhaka, mai shekara 27 mukaminsa na kaftin ya shafi bacin ran da ya nuna tsakanin da magoya baya a wasan da Arsenal ta tashi 2-2 da Crystal Palace a ranar 27 ga Oktoba.

"Na gana da shi kuma na shaida ma sa cewa yanzu ba shi ba ne kaftin," in ji Emery

"Kuma ya amince da matakin da na dauka, domin dole na dauki mataki," in ji Emery

A watan da ya gabata an yi wa dan wasan ihu a yayin da yake fita filin Emirates, matakin da ya sa ya rufe kunnuwansa tare da tube riga.

Xhaka, dai ya taimakawa Arsenal zuwa wasan karshe na lashe kofin League a 2018 da kuma zuwa wasan karshe a gasar zakarun Turai ta Europa a bara.
BBC.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment