Monday, 11 November 2019

An Yi Wa Wani Sojan Nijeriya Yankan Rago

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Yusif Baba Waziri Birnin Kudu ya rasu ne sakamakon wasu da ba a san su waye ba suka yi masa yankan rago a garin Jama'are dake jihar Bauchi. 


Kafin  Rasuwar sa ma'aikacin sojan ruwa ne na Nijeriya. Kuma an bayyana shi a matsayin jajirtaccen soja ne mai kwazo akan aikinsa.

Yana aiki domin kasar sa don samun zaman lafiya. Sannan kuma ta fannin mu'amala da sauran mutane yana da fara'a da girmama na gaba da shi da mutunta mutane. 

Allah ya jikan sa ya gafarta masa, ya sa Aljanna ce makomar sa.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment