Tuesday, 5 November 2019

Ana ci gaba da rufe shagunan 'yan Najeriya a Ghana

Kungiyar `yan kasuwa ta Ghana GUTA ta ci gaba da garkame gwamman shagunan `yan Najeriya da karfi da yaji da ke Opera Square a birnin Accra.


Talata ce dai ranar karshe da kungiyar ta GUTA ta bai wa gwamnati da ta tilasta wa `yan kasuwar na kasashen waje bin dokar kasuwanci, ko su ci gaba da garkame shagunan kamar yadda suka gudanar a birnin Kumashi.

Chief Chukuemeka Nnaji shugaban kungiyar kasuwan Najeriya ta Ghana ya tabbatar wa da BBC lamarin.


Kawo yanzu dai kungiyar 'yan kasuwar ta Ghana ta rufe shaguna fiye da 100 na 'yan kasar waje da ke birnin Kumasi.


'Yan kasuwar na Ghana sun ce 'yan kasashen waje musamman 'yan Najeriya na gudanar da harkokin kasuwanci ba bisa ka'ida ba.

To amma 'yan kasuwar na Najeriya sun musanta ikrarin na 'yan Ghana.

Ana dai ganin garkame shagunan ba ya rasa nasaba da rufe iyakokin da Najeriya ta yi, al'amarin da ke ci gaba da tunzura wasu 'yan kasashen Afirka.

Gwamnatin Ghana ta nemi 'yan kasuwar na Ghana da su guji aikata abin da suke yi domin gudun hakan ka iya shafar alakar kasar da Najeriya.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake rufe wa 'yan Najeriya shaguna a Ghana.

Ko a watan Yuni ma sai da wasu mutanen da ba a san ko suwane ne ba suka rufe shagunan 'yan Najeriya 20 a birnin na Kumasi.

An kuma samu faruwar irin wannan al'amarin a birnin Accra.

Kungiyar 'yan kasuwar 'yan Nigerian mazauna Ghana sun bukaci 'yan uwansu da su kwantar da hankalinsu inda ta kara da cewa tana bakin kokarinta wajen warware matsalar.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment