Friday, 29 November 2019

Arsenal: An kori Unai Emery daga aikinsa

Kungiyar Arsenal ta bayar da sanarwar korar kocinta Unai Emery a yau Juma'a tare da dukkanin mataimakansa.


Tsohon dan wasan kungiyar Freddie Ljungberg ne zai maye gurbin Emery, wanda ya zama mataimakin Emery a watan Yuni, yayin da take ci gaba da neman koci na dindindin.

"Mun bayar da sanarwar cewa mun yanke hukuncin rabuwa da kocin tawagarmu Unai Emery da kuma mataimakansa," kungiyar ta bayyana.
Ta kara da cewa: "Muna godiya ta musamman ga Unai Emery da abokan aikinsa bisa jajircewarsu domin dawo da Arsenal kan turbar lashe kofuna kamar yadda muke bukata".

"Muna yi wa Unai fatan alheri a ayyukansa na gaba. An dauki matakin ne saboda irin sakamakon da aka rika samu wanda ba shi ne abin da ya kamata ba."

Gunners ba ta ci wasa ba a cikin bakwai da ta buga sannan kuma ta yi rashin nasara da ci 2-1 har gida a hannun Frankfurt a daren jiya a gasar Zakarun Turai ta Europa League.

Rabon da ta ci wasan Premier tun ranar 6 ga watan Oktoba kuma maki takwas ne tsakaninta da 'yan hudun farko a saman teburi.


Tuni Ljungberg ya karbi aikin horarwa a ranar Juma'a kuma kulob ya ce: "Muna da kwarin gwiwa kan Freddie Ljungberg domin ciyar da kungiyar gaba".

"Muna ci gaba da neman koci sannan kuma za mu bayar da wata sanarwa a nan gaba", in ji Arsenal.

Wadanda ake sa ran za su karbi aikin horar da kungiyar na dindindin sun hada da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino da mataimakin kocin Man City Mikel Arteta da tsohon kocin Juventus Massimiliano Allegri, sai kuma Eddie Howe kocin Wolves.

Arsenal ta kare a mataki na biyar a shekarar Emery ta farko bayan ya maye gurbin Arsene Wenger a watan Mayun 2018.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment