Tuesday, 5 November 2019

Ba za'a iya maganin matsalar satar mutane dan kudin fansa ba>>Inji wani Gwamna

Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya bayyana cewa ba zai taba yiyuwa a magance matsalar satar mutane dan kudin fansa ba a Najeriya saidai kawai a yi kokarin rage matsalar.Gwamnan ya bayyana hakane a yayin da wasu kungiyar Rotary ta kaimai ziyara a fadarshi dake birnin Fakwal inda yace.

Satar mutane dan kudin fansa ba za'a taba iya kawar da itaba a Najeriya saboda abin ya zama kasuwanci kawai abinda za'a iyayi  shine  rage yawan matsalar.

Gwamnan ya bayyana cew a lokacin da a yankin inyamurai kawai ake abin an rika mai kallon siyasa amma yanzu ya karade duka jihohin kasarnan kuma ana sace alkalai da manyan mutane. Dan haka akwai bukatar hadin kai dan magance matsalar.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment