Monday, 4 November 2019

Balotelli ya durma kwallo cikin 'yan kallo sannan ya fice daga filin wasa bayan da aka mai zagin wariyar launin fata

Tauraron dan kwallon kasar Italiya me bugawa kungiyar Brescia wasa, Mario Balotelli ya dauki kwallo da hannunshi ya dankarata cikin 'yan kallo bayan zagin wariyar launin fata da aka mai yayin wasasu da Verona.
Daga nan kuma Balotelli yayi yunkurin ficewa daga filin wasan inda 'yan wasan kungiyarshi dana Verona da sauran ma'aikata suka lallasheshi ya hakura ya tsaya.

Alkalin wasan ya dakatar da wasan na wasu 'yan mintuna inda aka yi sanarwar cewa idan aka samu cin zarafin nuna wariyar launin fata to za'a dakatar da wasan gaba daya.

Wani bidiyon da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta ya nuna yanda lamarin ya faru inda aka rika jin anawa Balotelli ihun biri.
Wasan dai ya kare Verona na cin 2-1 inda Balotelli ne ya ciwa kungiyarshi da Brescia kwallo1.

Bayan kammala wasan kocin Verona da shugaban kungiyar sun bayyana cewa ba'awa kowane dan wasan zagin wariyar launin fata ba in ma an yi su basu ji ba, sun bayyana cewa magiya bayansu basa zagin wariyar launin fata. Shugaban kungiyar yace idan mutum daya biyu ko uku sun yi zagin wariyar launin fata be kamata a ce gaba dayan magoya bayan kungiyar bane suka yi.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment