Sunday, 3 November 2019

Banda Maketatan dake cikin hukumar kwallon kafa da dana ya lashe kyautar Ballon d'Or da yawa>>Mahaifiyar Cristiano Ronaldo

Mahaifiyar tauraron san kwallon kafar kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo watau, Dolores Aveiro ta bayyana cewa in banda wasu maketata dake cikin kungiyar kwallon kafa ta Duniya da dan nata ya lashe manyan kyautukan kwallo da yawa.Ronaldo dai na da kyautar gwarzon dan kwallon kafar Duniya ta Ballon d'Or har guda 5 kuma yana cikin wadanda ake ganin zasu iya lashe kyautar ta bana.

Da take hira da wani gidan talabijin na kasar Portugal, Dolorez ta bayyana cewa wasu maketatane a hukumar kwallon kafa suke hana dan nata lashe kyautukan da ya kamata a bashi.

Tace da ace dan nata daga kasar Ingila ko sifaniya ya fito da ba'a rika mai abinda ake mai ba.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment