Monday, 4 November 2019

Bayer Munich ta kori kocinta bayan shan ci 5-1

Bayern Munich ta sallami kocinta Niko Kovac bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun Frankfurt da ci 5-1 a Bundesligar Jamus wasan mako.


Kovac ya bar Bayern Minich a mataki na hudu kan teburi, maki hudu kenan tsakaninta da Borussia Monchengladbach, wadda ke ta farko a saman teburi.

Tsohon dan wasan tsakiyar Croatia mai shekara 48, Kovac ya fara jan ragamar kungiyar Bayern a watan Yulin shekarar 2018.

Kovac ya ya yi nasara a wasa 45 cikin 65 da ya ja ragamar Bayern, sai dai abin kunyar da ta yi shi ne karo na farko mafi muni a cikin shekara 10 a gasar Bundesliga.

Bayan wasan ne Kovac ya bayyana cewa ba shi da tabbas kan makomarsa a kungiyar.

"Na san yadda harkar take, kuma ba na jin ko dar saboda kashin da muka sha," Inji Kovac.

Ya kara da cewa: "Ra'ayina ba shi da wani amfani domin wadanda suke yanke hukunci su ne za ka tambaya game da halin da ake ciki."

Mataimakin kocin Bayern din Hansi Flick shi ne zai wakilci kungiyar a wasan da za ta fafata da Olympiacos a gasar Zakarun Turai ta Champions League ranar Laraba da kuma wanda za ta kece raini da Borussia Dortmund ranar Asabar.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment