Saturday, 9 November 2019

Benzema ya kafa muhimman tarihi a Real Madrid: Messi ya ci kwallaye 3 shi kadai a wasan da Barca ta wa Celta Vigo 4-1

Kngiyar kwallin kafa ta Real Madrid ta lallasa Eibar da ci 4-0 a wasan da suka buga yau na gasar cin kofin Laliga inda Benzema ya ci kwallaye 2, Ramps ya ci 1, Valverde ya ci 1.Da kwallayen da yaci yau, Benzema ya ciwa Madrid jimullar kwallaye 157 kenan inda ya zarta tsohon dan wasan kungiyar, Puskas me kwallaye 156, sanan Benzema ya zama na 6 da yafi ciwa Madrid kwallaye a gasar Laliga.

Kocin Madrid, Zidane ya bayyana cewa ya kamata Faransa ta saka Benzema cikin wanda zasu buga mata kwallo, a kakar wasan data gabata, Benzema ya ci kwallaye 30 a bana kuma ya ci 12.

Ita Barcelona ta lallasa Celta Vigo da ci 4-1 inda Messi ya ci kwallaye 3 shi kadai wanda 2 daga ciki duk kayatattun bugun tazarane.

Sai kuma Busquest da ya ci kwallo ta 4.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment