Thursday, 7 November 2019

Boko Haram sun kashe sojoji 10 da raunata wasu 9 bayan harin kwantan Bauna

Wani rahoto daya fito daga kamganin dillancin labarai na AFP ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kaiwa Sojojin Najeriya harin kwantan bauna inda suka kashe sojoji 10 da kuma raunata wasu 9.

Rahoton yace lamarin ya farune a garin Damboa yayin da Sojojin ke yawan Sintiri a jiya,Laraba.

Hakanan wasu sojoji 12 sun bace bayan hararin kamar yanda wani soja da baya son a ambaci sunanshi ya bayyanawa kafar watsa labaran AFP.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment