Tuesday, 5 November 2019

Buhari ya taka wa kamfanonin mai burki kan rijiyoyin mai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudirin yi wa dokar rijiyoyin cikin teku da tsarin kwangilar samar da mai ta doron kasa gyaran fuska wadda ta fayyace yadda za a kasa ribar mai da ake siyarwa fiye da dala 20 a kasuwar duniya.


Kimanin makonni biyu dai ke nan majalisar dokokin kasar ta amince da kudirin inda ta mika ga fadar shugaban kasa domin rattaba hannu kan kudirin domin zamowa doka.

Shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Litinin cewa ya rattaba hannu kan kudirin dokar:Buhari ya ce "Na amince da kudirin da ya yi wa dokar rijiyoyin cikin teku da na kan tudu gyaran fuska. Wannan ba karamar nasara ba ce ga Najeriya; zan yi amfani da wannan dama wajen mika godiyata ga majalisar dokokin kasar la'akari irin hadin kan da majalisar ta bayar."

Tun dai a shekarar 1999 dokar take, to sai dai sakamakon rashin cimma matsaya tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanonin mai na kasashen duniya kan yi mata kwaskwarima ya sa ba a iya aiwatar da ita ba.

Dokar dai ta yi bayani kan yadda Najeriya za ta amfana daga tashin farashin gangar mai daga dala 20 a kasuwar duniya, inda ta fayyace yawan abin da kasar za ta samu.

A baya-bayan nan gwamnatin kasar ta sha maka kamfanonin mai na kasashen waje a kotu bisa yin ruf-da-ciki kan kudaden da ya kamata su shiga aljihun kasar a lokutan tashin farashin man.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment