Sunday, 3 November 2019

Buhari Zai Iya Neman Zarcewa Kan Mulki A Karo Na Uku>> Buba Galadima

Tsohon shakikin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da kada su yi mamaki idan Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi kujerar shugabncin kasa a shekarar 2023. 


Galadima, wanda a halin yanzu aboki ne ga Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa karkshin jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya ce akwai masu angiza shugaban kasar don ya kara neman zarcewa kujerarsa. 

A tattaunawar da yayi da jaridar The Sun, Galadima ya yi ikirarin cewa, Buhari ya killace ma'aikatar shari'a, don haka ne ya yi wucewar sa zuwa Saudiyya ana gobe kotun koli za ta duba shari'ar sa da Atiku.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment