Thursday, 7 November 2019

CAKWAKIYA: Sunayen Hadiman Osinbajo Su 35 Da Shugaba Buhari Ya Kora

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori hadiman mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo har su 35 daga yin aiki a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa. 


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ta samu cikakkun sunaye hadiman wadanda mafi yawa daga cikinsu na hannun daman mataimakin shugaban kasar nan. 

Daga cikin jerin sunayen wadan da lamarin ya shafa su hada da Ajibola Ajayi, 'yar tsohon gwamnan jihar Oyo, Isiaka Abiola Ajimobi mataimaka wa Shugaban kasa (a ofishin mataimakin shugaban kasa) a fannin Shari'a. Ta kasance tsohuwar SA ga Shugaban kasa daga 2015 zuwa 2019.

Har ila yau a jerin suna akwai Lanre Osinbona, Babban Mataimaki na Musamman (SSA) a kan lamarin Fasahar Sadarwa  ICT; Imeh Okon, SSA akan Lantarki; Jide Awolowo, SA, akan Man Fetur da Gas; Gambo Manzo, SA a kan lamarin Siyasa da Edobor Iyamu, SSA, bangaren lamuran yankin Niger Delta.

Majiyoyi da dama daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da korar mataimakan, inda wasu daga fadar ke cewa hakan na da nasaba ne da kokarin da ofishin shugaban kasa ke yi na rage karfin ikon mataimakin shugaban kasa kamar yadda ya faru da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo bayan lashe zabensa a karo na biyu. 

Masana harkokin siyasa dai na cewa dukka wadannan dambarwa da ake samu tsakanin Ofishin shugaban kasa da mataimakinsa ba ya rasa nasaba da takarar shugaban kasa a 2023.  

An ruwaito cewa mataimakin shugaban yana da mataimaka sama da 80 wadanda suke taimaka masa a bangarori da dama na lamuran gwamnati.

A halin yanzu dai Yemi Osinbajo ya ya karbi takardun kora daga fadar shugaban kasa da aka yi wa hadiman nasa da suka fito daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, har sai shugaban kasa ya dawo domin ya ji dalilin yin hakan, inda maijiyar ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasan ya nuna rashin jin dadinsa matuka da faruwar haka. 

Wata majiya mai tushe ta kara bayyana cewa kora da aka yi wa hadiman bai shafi barin aiki ba, sai dai an raba su ne da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da rarrabasu zuwa ma'aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya daban daban. An kuma ruwaito cewa jami'an tsaron fadar shugaban kasa sun karbi dukkanin ID Card da zai bai wa wadan da aka koran ikon shiga fadar shugaban kasa kai tsaye.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment