Thursday, 28 November 2019

Champions League: Chelsea ta buga 2-2 da Valencia: Ajax ta lallasa Lille da ci 2-0

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta buga 2-2 da Valencia a wasan da suka yi na gasar cin kofin Champions League a daren jiya.Valencia ce ta fara cin Chelsea kwallo amma daga baya Chelsea ta rama hadda kari, kwallo ta biyu da Pulisic ya ciwa Chelsea wadda kuma itace kwallonshi ta farko a gasar ta Champions League, da farko Alkalin wasan yace yayi satar gida amma daga baya na'urar VAR ta tabbatar da ita.

Valencia ta samu bugun daga kai sai gola amma ta barar da damar saidai daga baya a minti 82 ta samu ta farke kwallon tata.

Tammy Abraham ya ji rauni a ciki inda aka fita dashi daga wasan amma Lampard yace yana tsammanin ba me tsanani bane.

Wasa na gaba da aka buga a jiya a rukunin H shine wanda Ajax ta Lallasa Lille da ci 2-1.

Dan wasan Ajax, Hakeem Ziyech ya haskaka sosai inda yaci kwallo ya kuma bayar aka ci sannan ya ci kwallo ta 2 amma aka kashe ta.

Wani lamari ya faru a lokacin wasan da ya dauki hankuka sosai inda inda wani yaro yayi kutse cikin fili ya je wajen Ziyech kuma Dan wasan ya rungumeshi.

Sauran wasannin Champions League na jiya sune:

Petersburg ta lallasa Lyon da ci 2-0

Sai Benfica da Leipzig da suka buga 2-2.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment