Wednesday, 6 November 2019

Champions League: Liverpool ta buga 21 da Genk: Haaland ya kafa tarihin da babu me irinshi

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta buga 2-1  da Kungiyar Genk a wasan da suka yi a daren jiya na gasar cin kofin Champions League. Wijnaldum da Chamberlain ne suka ciwa Liverpool kwallayenta.


Sai kuma wasa na 2 da aka buga a rukunun E tsakanin Napoli da Salzburg wada suka tashi da sakamakon kunnen doki watau 1-1.

Dan wasan Salzburg, haaland me shekaru 19 ne ya ci mata kwallon ta jiya, da wannan ya kafa tarihin zama dan wasan kwallo me shekaru kasa da 20 na farko da ya ci kwallaye 7 a kasar wasa daya na gasar Champions League, ya shiga gaban Raul da Kylian Mbappe da suka ci kwallaye 6 kowannensu a kakar wasa daya a gasar.

Sannan Haaland ya zama dan kwallo na farko da ya ci kwallaye 7 a wasanshi na farko a gasar wanda banda shi babu wanda ya ke da irin wannan tarihi saidai kasa da haka.

Hakanan ya zama dan kwallo na 4 da ya jera wasanni 4 na gasar farko daya fara bugawa a Champions League yana cin kwallaye a kowanne bayan Ze Carlos, Del Piero da Diego Costa.

Sauran wasannin da aka buga jiya, sune, Lyon ta wa Benfica 3-1 sai kuma Leipzig da tawa Petersburg 2-0
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment