Wednesday, 6 November 2019

Champions League:Barcelona ta buga 0-0 da Slavia Parague: Dortmund ta ci Inter 3-2: Messi ya zubar da kyawawan kwallaye

Wasan da aka buga tsakanin Barcelona da Slavia Prague a na gasar cin kofin Champions League a daren jiya an tashi babu ci da sakamakon 0-0.Barca dai na kamfar cin kwallo wadda a karshen makon da ya gabata aka ga yanda ta sha kashi a hannun Levante da ci 3-1.
Messi ya barar da damarmaki sosai a wasan na yau wanda ya kamata ace ya ciwa Barca kwallo,kwallo ta farko da ta fi daukar kanhalin mutane itace wadda Messin ya ja kuma ga Griezmann wanda da ya bashi kwallon ya fishi damar ci amma Messin ya bugata ta daki karfen raga ta fita waje, da dama sun caccaki messi akan wannan kwallon.

Sai kuma kwallon dan Ansu Fati ya baiwa Messi ita ma bai yi nasarar sakata a ragaba duk da cewa yana gaf da ragar.

Akwai kuma kwallon da aka baiwa Messi ya durmata sama.Dayan wasan da aka yi a rukunin F na gasar a jiya shine tsakanin Inter Milan da Dortmund wanda aka tashi Dortmund na cin 3-2.

Hakimi ne ya ciwa Dormund kwallaye 2.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment